Najeriya

Rashin isassun kudade ke takaita ayyukan jami'an tsaro - Buratai

Babban Hafsan Sojan Najeriya  Tukur Yusuf Buratai.
Babban Hafsan Sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai. Pulse.ng

Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya danganta matsalar tabarbarewar tsaron da ake fuskanta a sassan Najeriya, musamman a arewacin kasar da rashin isassun kudaden da ake warewa rundunar sojin kasar da sauran hukumomin tsaro.

Talla

Burutai ya bayyana haka ne yayin Karin bayani kan kasafin kudin tsaro ga kwamitin majalisun dokokin Najeriya kan fannin.

A cewar babban hafsan sojin, a shekarar bana ta 2019, rundunar sojin Najeriya za ta kasha naira biliyan 472 da miliyan 800 wajen gudanar da ayyukanta.

Kaso mafi yawa daga cikin kudin kuma za yi amfani da shi ne wajen samar da tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya, da kuma warware sauran matsalolin da ake fuskanta a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI