Najeriya

Alkalin-alkalan Najeriya ya yi murabus daga kujerarsa

Shugaba Muhammadu Buhari da  Walter Onnoghen
Shugaba Muhammadu Buhari da Walter Onnoghen lailasnews

Babban mai shari’a a Najeriya Walter Onnoghen ya aika wa shugaban kasar, Muhammadu Buhari da takardarsa ta murabus, sakamakon tuhumar da ake yi masa na kin bayyana kadarorin da ya mallaka da kuma boye asusun ajiyarsa.

Talla

Lauyan Onnoghen, Adegboyega Awomolo ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP cewa, tabbas alkalin-alkalan ya ajiye aikinsa tun a ranar Alhamis.

A karkashin doka ta 306 na kundin tsarin mulkin Najeriya, murabus din Onnoghen ya fara aiki nan take, yayinda masana ke kallon matakin da ya dauka a matsayin abinda yafi dacewa biyo bayan tuhumar da aka yi masa kan cin hanci da rashawa.

Ana ganin Onnoghen zai karbi kudin sallama da kadarar da ta kai ta Naira biliyan biyu da rabi da ya kunshi albashi har karshen rayuwarsa da gina masa gida a birnin Abuja da kuma biyan wasu ma’aikatan da za su ci gaba da yi masa hidima.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bayar da umarnin dakatar da Onnoghen ‘yan makwanni kafin fara gudanar da zaben shugabancin kasar a cikin watan Fabairu, abinda ya haifar da cece-kuce daga ciki da wajen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.