Najeriya

'Yan kunar bakin- wake sun kashe mutane 11 a Borno

Ana zaton 'yan matan da suka kai harin nada alaka da mayakan Boko Haram
Ana zaton 'yan matan da suka kai harin nada alaka da mayakan Boko Haram STRINGER / AFP

Akalla mutane 11 sun rasa rayukansu, yayinda 43 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin-wake da wasu ‘yan mata biyu suka kaddamar a wajen birnin Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya.

Talla

'Yan matan da ke da karancin shekaru kuma ake kyautata zaton alakarsu da Boko Haram, sun tayar da bama-baman da suka yi damara da su a Muna, mai tazarar kilmita biyar daga babban birnin Maiuduguri.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkaen rahoton da wakilnmu Bilyaminu Yusuf ya aiko mana daga Maiduguri.

'Yan kunar bakin- wake sun kashe mutane 11 a Borno

Hukumar bayar da agajin gaggauwa ta NEMA ta tabbatar da kai farmakin na kunar bakin-wake

A halin yanzu wadanda suka samu rauni a harin, na ci gaba da karbar magani a babban asibitin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI