Najeriya

"Sarakunan gargajiya na da hannu a rikicin arewacin Najeriya"

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali
Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali REUTERS/Paul Carsten

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali ya bayyana cewa, sabbin bayanan sirri sun nuna cewa, wasu manyan sarakunan gargajiya na da hannu a kashe-kashen da ake fama da su a wasu yankuna na arewacin kasar.

Talla

A wata sanarwa da ya aika wa Jaridar Premium Times, Ministan ya ce, sun gano cewa, sarakunan gargajiyar da ba a bayyana sunansu ba, na da hannu a hare-haren 'yan bindigar, amma ya lashi takocin cewa, za su fuskanci hukunci.

Ministan ya bukaci al’ummar jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da sauran sassan arewacin Najeriya da su tashi tsaye wajen bayar da goyon baya ga yunkurin gwamnati na magance tashin hankalin, lura da cewa, sojojin da ke filin-daga ba za su iya yakar maharan su kadai ba.

Hare-haren ‘yan bindiga sun kazanta a ‘yan kwanakin nan musamman a Zamfara, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.

Kazalika har yanzu kasar na fama da matsalar Boko Haram a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.