Najeriya

Majalisar Najeriya ta ware Naira biliyan 10 ga Zamfara

The Nigerian Senate
The Nigerian Senate venturesafrica

Majalisar Dattawan Najeriya ta tsayar da kudurin ware Naira biliyan 10 daga kasafin kudin 2019 domin kula da mutanen da hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a jihar Zamfara.

Talla

Majalisar ta dauki matakin ne bayan muhawarar da Sanata Kabiru Garba Marafa na jam’iyyar APC daga jihar Zamfara ya gabatar a ranar Laraba.

Marafa ya bukaci samar da kudaden tallafi domin agaza wa mutanen da rikicin jihar Zamfara ya raba da muhallansu ko kuma ya shafa.

Majalisar ta yi Allah-Wadai da kashe-kashen da ake fama da su a jihar, in da ta jinjina wa ‘yan Najeriya kan yadda suka yi fitar-dango domin nuna goyon bayansu ga al’ummar jihar.

Kazalika Majalisar ta koka kan yadda matsalar tsaro ta tabarbare a wasu sassan Najeriya da suka hada da Kaduna da Katsina da Sokoto da Filato da Benue da Taraba da sauransu.

Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya ce, akalla mutane dubu 3 da 500 ne suka rasa rayukansu cikin shekaru biyar sakamakon hare-haren ‘yan bindaga a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.