Najeriya

Sarakunan Zamfara sun kalubalanci Gwamnatin Najeriya

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali
Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali REUTERS/Paul Carsten

Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara da ke tarayyar Najeriya ta bukaci Ministan Tsaron Kasar, Mansur Dan Ali da ya bayyana sunayen sarakunan gargajiyar da ya ce, suna hada baki da ‘yan bindiga wajen kaddamar da farmaki kan al’umma.

Talla

Majalisar ta bayyana haka ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sarkin Anka kuma shugaban Majalisar, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, yayinda Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru ya karanta sanarwar bayan wani taron gaggawa da suka gudaar a birnin Gusau.

Majalisar ta bayyana cewa, muddn Ministan ya gaza bayanna sunayen sarakunan da ke hada baki da ‘yan bindigar, hakan na nufin cewa, akwai karya a zancensa, kuma wani yunkuri ne na bata sunan sarakunan.

A cikin makon nan ne, Ministan Tsaron ya bayyana cewa, sabbin bayanan sirri sun nuna cewa, wasu manyan sarakunan gargajiya na da hannu a kashe-kashen da ake fama da su a wasu yankuna na arewacin kasar da suka hada da Zamfara da Katsina da Sokoto.

Ministan ya bukaci al’ummar jihohin da sauran sassan arewacin Najeriya da su tashi tsaye wajen bayar da goyon baya ga yunkurin gwamnati na magance tashin hankalin, lura da cewa, sojojin da ke filin-daga ba za su iya yakar maharan su kadai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI