Najeriya-Amurka

Sojin ruwan Najeriya sun kame jiragen ruwa dauke da makamai

Rundunar Sojin ruwan Najeriya ta sanar da kama wasu jiragen ruwa guda biyu tare da mutane 19 da ke dauke da makamai kusa da gabar ruwan kasar.

Mutane 19 ciki har da 'yan Girka 3 da ba'amurke 1 da hadakar sojin ruwan Najeriya da Amurka suka kame dauke da makamai da Fetur din sata2019-04-18
Mutane 19 ciki har da 'yan Girka 3 da ba'amurke 1 da hadakar sojin ruwan Najeriya da Amurka suka kame dauke da makamai da Fetur din sata2019-04-18 NAN
Talla

Kwamandan rundunar sojin da ke kula da gabar ruwan, Kwamado Dickson Olisemenegor ya ce sun yi nasarar kama jiragen ne yayin wani aikin sintiri da suke yi tare da takwarorin su na Amurka.

Jami’in ya ce bayan makaman da aka samu a jiragen biyu, an kuma gano cewar jiragen na dauke da danyan mai na sata.

Cikin mutanen da aka kama har da 'yan kasashen Girka guda 3 da dan Amurka guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI