Najeriya

Mutane 22 sun mutu a sabon rikicin Tiv da Jukun

Mutane 22 sun mutu a sabon rikicin Tiv da Jukun a jihar Taraba
Mutane 22 sun mutu a sabon rikicin Tiv da Jukun a jihar Taraba Daily Trust

Akalla mutane 22 aka kashe a wani sabon arangama tsakanin 'yan kabilar Jukun da Tiv a karamar hukumar wukari da ke kudancin jihar Taraba ta Najeriya.

Talla

Tun a makwanni 3 da suka gabata ne dai al'umomin biyu ke yakar juna, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dinbin dukiyoyi.

Wani mazaunin yankin mai suna Bwacha David ya shaida wa Jaridar Premium Times cewa, 'yan tawayen Tiv sama da dari biyu ne suka kai musu harin ba-zata, in da suka cinna wa gidaje da dama wuta, suka kuma kashe mutane sama da 10.

Shi ma shugaban karamar hukumar Wukari, Adi Daniel ya tabbatar da harin.

Ko a ranar Litinin da ta gabata, mataimakin gwamnan jihar ya gana da shuagabannin  kabilun biyu domin rattaba hannu kan zaman lafiya, sai dai bayan ganawarsu aka sake kai hari a ranar Talata, baya ga na baya-bayan nanda aka kai a yau Jummu'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI