Najeriya

Maharan Kujuru sun bukaci Naira miliyan 60

Masu garkuwa da mutane sun bukaci Naira miliyan 60 a matsayin kundin fansar mutanen da suka sace a wurin shakatawar nan na musamman da ke Karamar Hukumar Kajuru a jihar Kadunan Najeriya bayan harin da suka kaddamar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu ciki har da wata ‘yar Birtaniya.

Wurin Shakatawar Kajuru da ke jihar Kadunan Najeriya
Wurin Shakatawar Kajuru da ke jihar Kadunan Najeriya Daily Trust
Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Aminu Sado daga Kaduna.

Maharan Kajuru sun bukaci Naira miliyan 60

'Yar Burtaniya mai suna Faye Mooney ta ziyarci jihar Kaduna ne domin yawon shakatawa tare da wasu mutane daga jihar Legas, in da lamarin ya rutsa da su.

Wata majiya daga Kaujurun ta ce, daya daga cikin masu garkuwar ya yi magana da masu kula da wurin shakatawar ta wayar tarho, in da ya bukaci a biya su Naira miliyan 60 kafin sakin mutane uku da ke ci gaba da zama a hannunsu.

A bangare guda, al’ummar yankin na Kajuru sun gudanar da zanga-zanga domin nuna bacin ransu kan yadda matsalar kashe-kashe da garkuwa da mutane ta yi kamari a Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI