Najeriya

Buhari na ziyara a jihohin Lagos da Borno

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFIHausa/Kabiru Yusuf

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na ziyara a jihar Legas domin kaddamar da wasu ayyukan da Gwamnan jihar mai barin gado ya yi, kafin ya wuce Borno a gobe Alhamis kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasar ta sanar.

Talla

Ayyukan da shugaban zai kaddamar sun hada da bude Cibiyar Kula da Lafiyar Uwa da Da, da hanyar sufurin motoci da ke unguwar Oshodi da kuma hanyar filin jiragen sama na kasa da kasa, yayinda kuma zai kaddamar da sabbin motoci 820 na jigilar fasinjoji.

Tuni aka girke jami’an tsaro musamman a wuraren da shugaban zai ziyarta a Lagos kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran kasar wato NAN ya rawaito

Jami’an sun hada da Sojin Sama da Kwastam da Jami’an Kula da Shige da Fice da Jami’an Tsaron Farin kaya da kuma Jami’an Kiyaye Hadduran Ababawan Hawa.

Ana saran shugaba Buhari ya ziyarci jihar Katsina a cikin mako mai zuwa, in da zai shafe mako daya kamar yadda majiya daga fadarsa ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI