Najeriya

Mutane 19 sun kone kurmus a hatsarin mota a Jigawa

Wani mummunan hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mahalarta bikin aure 19 a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya bayan tayar motarsu ta fashe, abinda yasa motar ta kauce hanya kafin daga bisani ta kama da wuta.

Hatsarin mota ya lakume rayuka 19 a jihar Jigawan Najeriya
Hatsarin mota ya lakume rayuka 19 a jihar Jigawan Najeriya Daily Post
Talla

Rahotanni na cewa, fasinjojin sun hada da mata da kananan yara da ke kan hanyarsu ta koma gida daga Bauchi, in da motar tasu ta yi hatsari a garin Gwaram Sabuwa mai tazarar kilomita 100 daga bababn birnin Dutse.

Shaidu sun ce, motar ta yi alkafura sannan ta kama da wuta, lamarin da yasa fasinjojin suka kone kurmus.

Rahotanni sun ce, motar mai daukar mutane 18, ta kwaso fasinjoji 40 gami da kananan yara, yayinda mutane 21 suka jikkata a hatsarin.

Daga cikin wadanda suka tsira da ransu har da wani karamin yaro da mahaifiyarsa ta cillo shi ta tagar motar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI