Najeriya

Shugaba Buhari na shirin tafiya London a yau

A wannan Alhamis shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi tafiya zuwa Birtaniya bayan kammala ziyara a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Shugaba Muhammadu Buhari da mukarrabansa a filin tashi da saukar jiragen sama a Abuja
Shugaba Muhammadu Buhari da mukarrabansa a filin tashi da saukar jiragen sama a Abuja RFI Hausa/Sadou
Talla

Mai maitamaka wa shugaban na musamman kan kafafen yada labarai, Femi Adesina ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau.

A ziyarar ta zai kai jihar Borno wani lokaci a yau, ana saran shugaban ya kaddamar da wasu ayyukan ci gaban al’umma musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma hanyoyi.

Wasu bayanai na cewa, a yayin ziyararsa a London, shugaban zai yi nazari game da sabbin Ministocin da zai yi aiki da su a sabuwar gwamnatinsa.

Bayan kammala ziyarar a Borno, shuganban zai kama hanya zuwa Birtaniya, yayinda ake saran dawowarsa Najeriya a ranar 5 ga watan Mayu mai zuwa.

Ko a ranar Laraba, sai da shugaban ya kai ziyara birnin Lagos domin kaddamar da wasu manyan ayyukan da gwamnatin jihar ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI