Najeriya

Majalisa ta gayyaci Babban Sufetan Najeriya kan kisan jama'a

Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci Babban Sufetan ‘Yan Sandan kasar Mohammed Adamu ya gurfana a gabanta, don jin dalilan da su sa yin garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe ke ci gaba da tsananta a kasar.

Babban Sufetan 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu
Babban Sufetan 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu Vanguard.ng
Talla

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Ike Ekweremadu, ya ce lalle matsalar satar mutane don yin garkuwa da su da kuma kashe su a wasu lokuta, ba bakon zance ba ne a Najeriya.

Ekweremadu ya ce, lura da yadda matsalar ke ci gaba da ta’azzara, akwai bukatar shugaban ‘yan sandan ya gurfana a gabansu a gaggauce.

Sanata Shehu Sani da ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ce ya gabatar da wannan bukata, bayan masu garkuwa da mutanen sun kashe Faye Mooney,  ma’aikaciyar agaji ‘yar Birtaniya da Matthew Oguche a wani wurin shakatawa da ke Karamar Hukumar Kajuru a Kudancin Kaduna.

Garkuwa da mutane din karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ke hana jama'a zirga-zirga cikin kwanciyar hankali musamman a wuraren da matsalar ta fi tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI