Najeriya

'Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji kan hanyar Abuja

Hanyar Kaduna da Abuja a Najeriya
Hanyar Kaduna da Abuja a Najeriya The Guardian Nigeria

Rahotanni daga arewacin Najeriya sun ce, masu sata da yin garkuwa da mutane sun sake bayyana akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka yi awon gaba da fasinjoji mai yawa.

Talla

Wani ganau da ya tsira, Mohammed Dambatta, ya shaida wa manema labarai cewa, masu garkuwa da mutanen sun tare hanyar ce da misalin karfe 3 na yammacin yau a Kurmin-Kare da ke karamar hukumar Kachia.

A cewar Dambatta, masu satar mutanen sun bude wuta ne kan mai uwa da wabi, lamarin ya tilasta wa motoci akalla 15 tsayawa, inda suka yi awon gaba da fasinjoji da dama.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, jami'an 'yan sanda suka ce, sun yi nasarar cafke Abubakar Ibrahim da ake zargi da kashe marigayi Sarkin Adara, Maiwada Galadima na Karamar Hukumar  Kajuru.

Matsalar garkuwa da jama'a domin karbar kudin fansa na ci gaba da addabar sassa da dama na Najeriya musamman jihohin Kaduna da Zamfara da Sokoto.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.