Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kai farmaki kan kauyen Adamawa

Rahotanni daga Jihar Adamawa da ke Najeriya sun nuna cewar, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyen kan Kuda dake Jihar Adamawa, inda suka kashe mutane 21, tare suka kona gidajen garin.

Wasu Iyalai da suka tserewa hare haren Boko Haram daga garin Michika a jihar Adamawa. 31/1/2015.
Wasu Iyalai da suka tserewa hare haren Boko Haram daga garin Michika a jihar Adamawa. 31/1/2015. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mazauna Yankin sun ce maharan sun kai harin ne cikin motoci guda 4 da tarin Babura, abinda ya sa mutanen garin da dama suka tsere.

Maina Ularama, wani shugaban al’ummar garin, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, mayakan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, yayin da Paul Waramulu, shima mazaunin garin yace kashi biyu bisa uku na kauyen ya kone kurmus.

Kauyen Kuda na karamar hukumar Madagali mai nisan kilomita 285 daga birnin Yola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI