Najeriya-Saudiya

Najeriya ta yi nasarar karbo dalibar da Saudiya ta tsare

Zainab Habibu tare da jami'an Diflomasiyar Najeriya.
Zainab Habibu tare da jami'an Diflomasiyar Najeriya. Premium Times Nigeria

Gwamnatin Najeriya ta yi nasarar karbo dalibar kasar Zainab Habibu, da gwamnatin Saudiya ta tsare bisa zarginta da safarar miyagun kwayoyi.

Talla

Hukumomin Saudiya sun tsare Zainab, daliba a Jami’ar Maitama Sule da ke Kano, bayan gano wasu kwayoyin Tramadol a Jakarta, wadanda ta ce wasu bata gari ne suka saka ba tare da saninta ba.

To sai dai daga bisani bayan gudanar da bincike a filin jirgin saman Malam Aminu Kano inda Zainab ta tashi zuwa Saudiya tare da Mahaifiyarta da kuma ‘yar uwarta, sai jami’an NDLEA, wato hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi suka gano cewa, shakka babu, sakawa dalibar kwayoyin aka yi ba tare da ta sani ba, kuma tuni wadanda ake zargi suka shiga hannu.

hakan tasa shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki, bayyana kansa, da wasu sanatoci da suka hada da Kabiru Gaya, Sam Egwu, Baba Kaka, Abdullahi Adamu, da kuma Aliyu Wammako, a matsayin manbobin kwamitin da aka kafa don gudanar da bincike mai zurfi, kan al’amarin da ya faru ga Daliba Zainab da ta tsallake tarkon bata garin da suka kware wajen boye miyagun kwayoyi a jakunkunan matafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI