Isa ga babban shafi
Najeriya

Magu ya zargi wasu gwamnoni da haddasa karuwar matsalolin tsaro

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC Ibrahim Magu.
Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC Ibrahim Magu. reuters.ng
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC Ibrahim Magu, ya zargi wasu gwamnoni a kasar da haddasa karuwar rashin tsaro a jihohinsu, domin samun karin kudaden da ake warewa don magance matsalolin tsaron.

Talla

Magu ya bayyana zargin ne yayin wani taro a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja, inda ya gabatar da jawabi kan yaki da cin hanci da rashawa, da kuma amfani da kudi wajen haddasa matsalolin tsaro a kasar.

Cikin jawabin nasa, Magu ya ce babu shakka akwai alaka mai karfi tsakanin matsalolin cin hanci da rashawa, garkuwa da mutane da satar dabbobi, da kuma sauran ayyukan ta’addanci da ke addabar sassan Najeriya.

Dangane da batun ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar kuwa, shugaban na EFCC, ya zargi ‘yan siyasar da suka jagoranci yankin da haddasa talauci tsakanin al’ummarsu sakamakon cin hanci da rashawa, matsalar da ta baiwa ‘yan ta’adda damar jan ra’ayin matasa cikin sauki.

A bangaren kudancin Najeriya kuwa, Ibrahim Magu ya kara da cewa ya kadu matuka da irin tarin dukiyar da wasu marasa kishin kasa suka sace daga karkashin hukumar kula da raya yankin Niger Delta mai arzikin mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.