Yan bindiga sun kai hari kan makarantar mata a Zamfara
Wallafawa ranar:
Gungun ‘yan bindiga sun kai hari kan makarantar sakandaren mata ta kwana da ke garin Moriki a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a Najeriya cikin daren ranar Laraba, inda suka yi awon gaba da wasu mutane.
Tuni dai gwamnatin Zamfara ta hannun mai bata shawara kan harkokin yada labarai, Ibrahim Dosara, ta tabbatar da kai harin, wanda ta ce babu wanda ya rasa ransa, sai dai ‘yan bindigar sun sace wasu mata 5, ma’aikatan makarantar.
Wani mazaunin garin na Moriki da muka tuntuba ta wayar hannu, ya tabbatar da cewa babu dalibai cikin wadanda ‘yan bindigar suka sace, sai dai ya ce adadin ma'aikatan makarantar da akai awon gaba da su ya kai 6.
An dai kwashe tsawon lokaci, jihar Zamfara na fama da hare-haren ‘yan bindiga, wadanda suka yi kamari cikin shekarar nan ta 2019, duk da cewa jami’an tsaro sun tashi tsaye wajen murkushe matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu