Najeriya-MDD

Buhari ya nemi taimakon MDD kan 'yan gudun hijira

Shugaba Muhammadu Buhari tare da Maria Fernanda Espinosa ta Majalisar Dinkin Duniya
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Maria Fernanda Espinosa ta Majalisar Dinkin Duniya RFI Hausa/Bashir

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen duniya wajen tallafa wa tarin 'yan gudun hijirar da kasar ke fama da su da kuma lalacewar kayan more rayuwa.

Talla

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da shugabar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na zama 73, Maria Fernanda Espinosa wadda ta ziyarci kasar.

Shugaban Najeriya ya ce, yanzu haka kasar na fama da akalla yara wadanda basu san iyayensu ko kuma in da suka fito ba, sakamakon rikicin Boko Haram da ya jefa mutane yankin cikin tashin hankali.

Buhari ya kuma tabo batun tafkin Chadi da kuma yunkurin sake janyo ruwa daga kasar Congo zuwa cikinsa domin farfado da rayuwar mutane sama da miliyan 30 da suka dogara da shi domin rayuwa da sana’oinsu.

Shugabar babban zauren majalisar Maria Espinosa ta yaba wa shugaba Buhari kan shugabancin kungiyar ECOWAS da Tafkin Chadi da kuma rawar da dakarun Najeriya ke takawa wajen ayyukan samar da zaman lafiya a kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.