Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta yi raddi kan ikirarin yawaitar rasa rayukan 'yan Najeriya a zamaninta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo tare da jagororin jam'iyyar APC Adams Oshoimhole da Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo tare da jagororin jam'iyyar APC Adams Oshoimhole da Bola Ahmed Tinubu. ayo Omoboriowo/Nigeria Presidency/Handout via Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP ta yi watsi da ikirarin cewa rayukan ‘yan Najeriya sun fi salwanta a zamanin mulkin gwamnatocinta da suka gabata da adadi mafi yawa, idan aka kwatanta da na wasu gwamnatocin, musamman ta APC da ke mulki a yanzu.

Talla

PDP ta maida martani ne kan kalaman da kakakin shugaban Najeriya malam Garba Shehu ya furta, yayin zantawa da wata kafar yada labarai a kasar dangane da karuwar matsalolin tsaro musamman hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane, inda ya ce, girmamar matsalolin bai kai yadda aka gani a karkashin gwamnatocin jam’iyyar PDP da suka wuce ba.

Garba Shehu ya kuma kara da cewa sace Magajin garin Daura Alhaji Musa Uba, wanda suruki ne ga dogarin shugaban Najeriya, kanal Muhammed Abubakar da ‘yan bindiga suka yi a ranar Larabar makon da ya gabata, ya nuna cewa jami’an tsaro ba sa fifita wani yanki fiye da wani, dangane da daukar matakan tsare rayukan al’umma.

Sai dai yayin da take maida raddi, PDP ta bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da ta daina kokarin kamantawa ko kiyasta adadin rayukan ‘yan kasar da suka salwanta a karkashinta da na gwamnatocin da suka gabata.

A cewar babbar jam’iyyar adawar, kamata yayi gwamnatin ta yanzu ta yi da gaske wajen murkushe matsalolin tsaron da ‘yan Najeriya ke fuskanta, zalika ya kamata gwamnatin APC ta dauki sace Magajin garin Daura da ‘yan bindiga suka yi a matsayi cin fuska da kuma kalubale gareta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.