Najeriya-Kano

Shugaban Majalisar Kano zai rika karbar fansho na har abada

Majalisar Dokokin Jihar Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano premiumtimes

Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke Najeriya ta amince da wata doka wadda za ta bai wa Kakakin Majalisar da Mataimakinsa damar karbar fansho daga asusun gwamnatin jihar har iya rayuwarsu.

Talla

Sabuwar dokar ta kuma kunshi daukar nauyin shugabannin Majalisar zuwa kasashen waje domin kula da lafiyarsu da kuma basu sabuwar mota duk bayan shekaru 4.

Wannan mataki na zuwa ne kasa da makwanni biyu bayan Majalisar Jihar Bayelsa ta amince da irin wannan doka, wadda Gwamnan jihar ya yi watsi da ita, yana mai cewar ba zai sanya hannu akai ba, sakamakon korafe -korafe daga ciki da wajen Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.