Najeriya

Majalisar Kano ta amince da dokar kirkirar sabbin masarautu 4

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu. Reuters

Majalisar dokokin Kano, ta kada kuri’ar amincewa da dokar kafa ma’aikatar kula da mulki da masarautun gargajiya, matakin da ya bada damar aiwatar da kudurin kirkirar sabbin masarautu guda hudu masu daraja ta daya a jihar ta Kano.

Talla

Garuruwan da za a nada sabbin Sarakunan masu daraja ta daya sun hada da Gaya, Karaye, Bichi da kuma Rano.

A cewar wadanda suka goyi bayan kudurin, kirkira ko karfafa masarautun garuruwan zuwa daraja ta daya, zai bada muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban tattalin arziki da kuma karfafa tsaro ga mazauna yankunan.

A makwanin da suka gabata majalisar dokokin jihar Kano ta kafa wani kwamiti da ta dorawa alhakin rage karfin masarautar Kano ta hanyar nada karin sabbin Sarakuna guda hudu masu daraja ta daya, sakamakon bukatar hakan da rahotanni suka ce wasu sun gabatarwa majalisar.

Gabannin amincewa da kudurin, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alkawarin sanya hannu kan dokar da zarar majalisar dokokin jihar ta amince da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.