Najeriya

Buhari ya jagoranci taro da hafsoshin tsaro sau 2 a mako 1

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Reuters/AFOLABI SOTUNDE

Karo na biyu cikin mako daya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jagorantar taro tsakaninsa da manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasar a Abuja.

Talla

A ranar Talata da ta gabata, aka soma taron na farko tsakanin Buhari da hafsoshin tsaron kasar, wanda ya mayar da hankali kan halin tsaro ke ciki a Najeriya.

Taron ya zo ne a dai dai lokacin da sassan Najeriya musamman a jihar Zamfara da makwabtanta da ke arewa maso gabashin kasar ke fama da hare-haren yan bindiga da kuma sata da yin garkuwa da mutane.

Tuni dai Shugaban Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa, matsalar tsaro a arewacin Najeriya ta fi muni a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari fiye da zamanin mulkin Goodluck Jonathan.

Farfesa Ango wanda tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ne da ke Zaria, ya ce, shugaba Buhari ba ya tabuka abin kirki wajen magance matsalar kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Kalaman Shugaban Kungiyar Dattawan na Arewacin Najeriya, martani ne kan ikirarin da kakakin shugaban kasar malam Garba Shehu ya yi, na cewa rayukan ‘yan Najeriya sun fi salwanta a zamanin mulkin gwamnatocinta da suka gabata da adadi mafi yawa, idan aka kwatanta da na wasu gwamnatocin, musamman ta APC da ke mulki a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI