Najeriya

Kano: Ganduje ya sa hannu kan dokar kirkirar karin masarautu 4

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayin sa hannu kan dokar kirkirar masarautu guda hudu masu daraja ta daya.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayin sa hannu kan dokar kirkirar masarautu guda hudu masu daraja ta daya. Solacebase

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sa hannu kan kudurin dokar kirkirar Karin masarautu masu daraja ta daya guda hudu a jihar.

Talla

A ranar Larabar da ta gabata, ta kada kuri’ar amincewa da dokar kafa ma’aikatar kula da mulki da masarautun gargajiya, matakin da ya bada damar aiwatar da kudurin kirkirar sabbin masarautu guda hudu masu daraja ta daya a jihar ta Kano.

Garuruwan da za a nada sabbin Sarakunan masu daraja ta daya sun hada da Gaya, Karaye, Bichi da kuma Rano.

Gabannin amincewa da kudurin dai, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alkawarin sanya hannu kan dokar da zarar majalisar dokokin jihar ta amince da ita.

Tuni dai jama'a daga fannoni daban daban suka soma tofa albarkacin bakins akan matakin na 'yan majalisu da kuma gwamnatin jihar ta Kano.

Dakta Tijjani Muhammad Naniya masanin Tarihi da ke, sashin nazarin Tarihi a jami'an Bayero da ke Kano, daya ne daga cikin dimbin jama'ar da suka yi tsokaci kan shirin na kirkirar karin masarautu guda hudu, masu daraja ta daya a jihar ta Kano.

Yayin tattaunawa da sashin Hausa na RFI, dakta Tijjani Naniya ya bayyana gaggauta amincewa da kudurin dokar da majalisar ta yi, a matsayin kuskure babba, domin kamata yayi ta soma bin tsarin da ya dace na soma tuntubar jagororin al'umma da suka hada da Dattawa, 'yan siyasa, Malamai da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Farfesa Tijjani Muhammad Naniya kan matakin gwamnatin Kano na raba masarautar jihar zuwa gida 4

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI