Najeriya-Kano

An fara binciken Masarautar Kano kan rashawa

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu. Reuters

Rahotanni daga jihar Kano a Najeriya na cewa jami’an fadar masarautar Kano sun soma gurfana a gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar, don bada ba’asi kan yadda fadar ta kashe kudadenta tun daga shekarar 2013 kawo yanzu. Wannan matakin ya kara fito da tsamin dangantaka tsakanin gwamnatin jihar da Masarautar.

Talla

Dama dai tun farkon makon nan ne gwamnatin jihar Kanon karkashin hukumar ta aika wa masarautar wasikar gayyatar wasu jami’anta, a ci gaba da binciken yadda fadar ta yi kashe kudaden.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin Kanon ta tabbatar da dokar kara yawan masarautu a jihar. Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Wakilinmu Abubakar Isa Dandago daga jihar ta Kano

Rahoto kan binciken Masarautar Kano

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI