Kano

Kanawa sun yi wa Sarki Sunusi tarba ta musamman

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta ce, ba za ta taba sauka daga matsayinta ba kan dokar sabbin masarautun da ta kirkiro guda hudu a daidai lokacin da mai martaba Sarki Sanusi na biyu ya dawo daga aikin Umra a kasar Saudiya, yayinda dubun-dubatan Kanawa suka yi masa kyakkyawar tarba.

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu. Insidearewa
Talla

A karshen mako ne dai Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika Sandar Girma ga sabbin sarakunan duk kuwa da umarnin da wata kotu ta bayar na dakatar da taron bikin. Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton da wakilinmu Abubakar Isah Dandago ya aiko mana.

Rahoto kan takaddamar kirkirar masarautu a Kano

Sarki Sunusi ya isa filin jirgin saman na Malam Aminu Kano a yammacin jiya Lahadi, inda masoyansa suka yi masa tarba ta musamman kuma cikin farin ciki, yayinda suka yi masa rakiya har zuwa fadarsa.

Rahotanni na cewa, Sarkin bai yi wani jawabi ba bayan isowarsa Najeriya daga Saudiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI