Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta tsaida ranar zama kan bukatar dakatar da rantsuwar Buhari

Kotun sauraron kararrakin zaben Najeriya za ta saurari bukatar neman dakatar da bikin rantsar da shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Kotun sauraron kararrakin zaben Najeriya za ta saurari bukatar neman dakatar da bikin rantsar da shugaban kasar Muhammadu Buhari. The Guardian
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Kotun sauraron kararrakin zaben Najeriya da ke Abuja, ta tsaida 22 ga watan Mayu, a matsayin ranar da za ta saurari bukatar da aka gabatar gabanta, ta neman dakatar da bikin rantsar da shugaban kasar Muhammadu Buhari kan wa’adi na biyu.

Talla

Dan takarar jam’iyyar HDP Ambrose Owuru da kuma shugabancin jam’iyyar ne suka garzaya kotun, inda suke kalubalantar rashin basu damar shiga zaben shugabancin Najeriya da hukumar INEC tayi a watan Fabarairu.

Sabon yunkurin kalubalantar nasarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na zuwa ne watanni 2 bayan da dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar NRM Usman Ibrahim Alhaji, ya garzaya kotu inda ya shigar da karar shugaba Buhari da dan takarar PDP Atiku Abubakar bisa karya dokar kashe kudade fiye da ka’ida yayin yakin neman zabensu, tare da bukatar soke zaben shugabancin kasar da ya gudana a watan Fabarairu.

Mai shigar da karar ta hannun lauyansa mai suna, Ofou Ezekiel, ya zargi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar dan takarar PDP da kashe sama da naira biliyan 1, yayin yakin neman zabensu, matakin da ya ce ya saba doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.