Najeriya

Kotu ta soke sabbin masarautun da aka kirkiro a Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu vanguard

Babbar kotun jihar Kano da ke Najeriya ta soke nadin sabbin sarakunan da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi, inda ta ayyana matakin a matsayin wanda ya saba wa doka, yayinda ta bukaci a koma kan tsarin da ake kai kafin ta kammala sauraren karar da aka shigar a gabanta. 

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Masu Zaben Sarki a masarautar Kano sun shigar da karar Ganduje a gaban kotun domin kalubalantar matakinsa na kirkirar sabbin masarautu hudu.

Masu Zaben Sarkin da suka hada da Sarkin Dawaki, Maituta Alhaji Bello Abubakar da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan da Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani da Makaman Kano, Alhaji Sarki Ibrahim Makama na kalubalantar Ganduje a gaban babbar kotun jihar.

Har ila yau, Masu Zaben Sarkin , sun shigar karar shugaban Majalisar Dokokin jihar, Kabiru Alhassan Rurum da ita kanta gwamnatin jihar da kuma sabbin sarakunan Gaya da Rano da Bichi da Karaye da Gandujen ya nada.

Ana saran wadanda ake zargin su bayyana a gaban kotun cikin kwanaki 21 da samun takardar kira daga kotun.

Masu Zaben Sarkin sun ce, dokar kirkirar sabbin masarautun ta yi hannun riga da tarihin masarautar Kano.

Masu Zaben Sarkin sun dauki lauyoyi 17 da kuma wasu manyan lauyoyi masu matsayin SAN su bakwai domin kalubalantar Ganduje.

Gabanin wannan lokaci dai, wata kotu da ke zama a Ugogo ta umarci Gwamnan jihar da ya dakatar da shirinsa na mika takardun nadi da sandar girma ga sabbin sarakunan na Gaya da Rano da Bichi da kuma Karaye.

Kirkirar sabbin masarautun ta haifar da cece-kuce a ciki da wajen Kano, inda wasu ke alakanta matakin da siyasa, yayinda wasu suka yi madalla da haka, wasu kuwa suka nuna adawarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI