Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kai farmaki kan wasu kauyukan jihar Katsina

'Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a kauyukan jihar Katsina.
'Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a kauyukan jihar Katsina. Information Nigeria
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Rahotanni daga Najeriya sunce ‘yan bindiga sun kai farmaki kan wasu kauyukan karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina, inda suka hallaka akalla mutane 20.

Talla

Farmakin da ‘yan bindigar suka kai cikin daren ranar Talatar da ta gabata, ya shafi kauyukan da ke iyaka da jihar Zamfara, wadanda suka hada da Karya, Dan Sabau da kuma Dan Marke.

A lokacin da yake tabbatar da kai harin, kamar yadda jaidar Daily Trust da ke Najeriya ta rawaito, Kantoman mulkin karamar hukumar ta Kankara Anas Isa ya ce, ‘yan bindigar da suka zo da adadi mai yawa da ya zarta na jami’an tsaron da ke yankin, sun bude wuta nan take kan jama’a, inda suka yi awon gaba da dabbobi da dama.

Anas Isa ya kara da cewa yanayin yawaitar duwatsun da ke yankin da rashin kyawun hanya, ya sanya jami’an tsaro gaza cimma maharan har zuwa lokacin da suka tsere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.