Najeriya

Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane 93

Wasu tarin makamai da kuma masu garkuwa da mutane da rundunar 'yan sandan Najeriya ta kame.
Wasu tarin makamai da kuma masu garkuwa da mutane da rundunar 'yan sandan Najeriya ta kame. The Nation

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kame wasu mutane 93, bisa kyautata zaton suna daga cikin ‘yan bindigar da suka addabi jama’a da sata da kuma yin garkuwa da mutane, a jihohin Niger, Katsina da kuma Kaduna, musamman akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan DCP Frank Mba, ya ce sun yi nasarar damke ‘yan bindigar ne, bayan shafe makwanni biyu suna kai samame kan maboyar maharan lokaci guda a jihohin na Kaduna, Katsina da kuma Niger.

Yayin bayyana ‘yan bindigar ga jama’a a garin Katari, da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, DCP Frank Mba, ya ce sun yi nasarar kwace tarin makaman da suka kunshi bindigogi kirar AK47 guda 35, bindigogi kirar gida 21, makamin roka da aka fi sani da ‘rocket launcher’ a turance, da kuma harsasai sama da 500.

Sauran kayayyakin da aka samu a hannun ‘yan bindigar sun hada da kakin sojoji, karamar bindiga kirar waje, da kuma takardun kudin dalar Amurka dubu 60 amma na Jabu.

Daga cikin mutanen da suka shiga komar jami’an tsaron har da wani da ke kiran kansa da malami, wadda yace shi baya sata ko yin garkuwa da mutane, sai dai taimakawa ‘yan bindigar da magungunan asiri domin samun Sa’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI