An samar da dokar kisa kan masu sace jama'a a Katsina
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Aminu Masari ya sanya hannu kan dokar Penal Code da aka yi kwaskwarima wadda kuma ta bayyana satar jama’a da shanu a matsayin manyan laifukan da suka cancanci hukuncin kisa.
Dokar ta kuma amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu yi wa mata fyade.
A yayin gabatar da jawabi, Gwamna Masari ya ce, jihar Katsina na fama da matsalar tsaro, abinda ya sa aka yi wa dokokin jihar gyarar fuska.
Kazalika Gwamnan ya bayyana fatan cewa, matakin da suka dauka a yanzu, zai tsawatar da mutanen da ke da shawa’ar shiga harkar sace-sacen jama’a domin karbar kudin fansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu