Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton hallaka dakarunta

Wasu dakarun sojin Najeriya a jihar Borno.
Wasu dakarun sojin Najeriya a jihar Borno. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Rundunar sojin Najeriya, ta musanta rahoton da wasu kafafen yada labarai suka bayyana, da ke cewa mayakan Boko Haram sun hallaka dakarun kasar 25, a wani farmaki da suka kai musu a jihar Borno.

Talla

Rahoton dai ya ce mayakan na Boko Haram sun kaiwa sojin Najeriyar farmaki ne, a lokacin da suke kan rakiyar fararen hula akan hanyar Damboa zuwa Biu, yayinda suke aikin kwashesu daga wasu yankuna, a ranar asabar da ta gabata.

Sai dai kakakin rundunar sojin Najeriyar, kanal Sagir Musa, ya bayyana rahoton a matsayin labari maras tushe da aka kago.

A ranar Larabar makon da ya gabata, kungiyar Boko Haram da ta yiwa IS reshen Afirka Ta Yamma mubaya’a, ta dauki alhakin wani hari, da ta ce ta kashe sojojin Najeriya 20, sannan ta saki wani hoton bidiyo da ke nuna yadda ta halaka wasu karin sojojin na Najeriya 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.