APC ta kori tsohon gwamnan jihar Zamfara
Wallafawa ranar:
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kori tsohon gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari, saboda jefa jam’iyyar cikin rudanin da yayi, na rasa baki dayan nasarorin da ‘yan takarar jam’iyyar suka samu a zabukan 2019, inda kotu ta mikawa PDP nasarorin.
APC ta kuma kori mataimakin shugabanta na yankin Arewacin Najeriya Lawal Shu’aibu, saboda samunsa da laifin hada baki da tsohon gwamnan na Zamfara, wajen yiwa jam’iyyar zagonsa yayin gudanar da zaben fidda gwanin ‘yan takararta a jihar, wanda ya sabawa ka’ida.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC reshen Zamfara, Alhaji Surajo Garba Mai Katako, ta ce an yanke shawarar korar tsohon gwamnan da kuma mataimakin shugaban jam’iyyar na arewacin Najeriya, yayin taron da suka yi a garin Gusau.
Sanarwar jam’iyyar ta APC ta kara da cewa, a ranar Alhamis mai zuwa bayan bikin Salla karama, za ta mikawa shugabancinta na kasa sakamakon matakin da ta dauka a hukumance.
A karshen watan Mayu kotun kolin Najeriya ta yi watsi da 'Yan takarar Gwamna da 'yan Majalisu a matakin tarayya da jiha na Zamfara, wadanda Jam’iyyar APC ta gabatar a zaben da akayi wannan shekara saboda zargin cewar Jam’iyyar ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba kamar yadda hukumar zabe ta gindaya.
Wannan hukunci ya nuna cewar jam’iyyar PDP ce za ta karbe kujerar Gwamna da na 'yan Majalisun saboda ita ta zo ta biyu a zaben da ya gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu