Najeriya

Majalisar Kaduna ta amince da dokar tantance masu wa'azi

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai. REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar dokokin jihar Kaduna, ta amince da wata sabuwar dokar sa ido kan malamai masu wa’azi daga bangaren Musulmi da Kirista.

Talla

Aikin dokar shi ne tattance malamai da kuma fastocin da ya kamata su rika yin wa’azi, sai kuma basu lasisi a matsayin shaidar amincewar gwamnati.

Zalika a karkashin dokar, duk wanda aka samu da laifin kunna wa’azi, ko gabatar da shi, ta hanyar amfani da na’urar amsa kuwwa a masallaci ko mujami’a, daga misalin karfe 11 na dare zuwa 4 na safe, zai fuskanci hukuncin biyan tarar da ba za ta gaza naira dubu 200 ba, ko kuma daurin akalla shekaru 2 ko ma sama da haka.

Dokar wadda makasudinta shi ne tabbatar da hadin kan mabiya addinai daban daban a jihar Kaduna, a baya ta fuskanci suka daga wasu malamai da fastoci, a lokacin da aka gabatar da kudurinta a zauren majalisar dokokin jihar ta Kaduna, a shekarar 2016.

Sabuwar dokar ta bada damar kafa kwamitin musamman na hadin gwiwa, da zai kunshi mabiya addinin Islama da na Kirista, zalika za’a kuma kafa rassan wannan kwamiti a dukkanin kananan hukumomin jihar 23, da zarar dokar ta soma aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI