Najeriya

Ahmed Lawan ya lashe zaben shugabancin Majalisar Najeriya

Sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmed Lawan.
Sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmed Lawan. premiumtimesng

Sanata Ahmed Lawan ya lashe kujerar shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya bayan ya samu kuri’u 79, abinda yasa ya doke abokin fafatawarsa, Sanata Ali Ndume wanda ya samu kuri’u 28.

Talla

Tuni Sanata Ndume ya taya Lawan murnar samun wannan nasara, inda ya yi musafaha da shi jim kadan da sanar da sakamakon zaben da sabuwar Majalisar ta 9 ta kada a ranar Talata.

Sabbin mambobin Majalisar sun kada kuri’unsu ne a sirce.

Sanata Lawan dai, shi ne wanda Jam’iyyar APC ke mara wa baya, yayinda jam’iyyar adawa ta PDP ta ce, za ta goya wa Ndume baya don ganin ya samu nasara.

Sanatoci 107 ne suka kada kuri’un na shugabancin majalisar kamar yadda akawun majalisar, Mohammed Sani-Omolori ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI