Najeriya

Gbajabiamila ya zama sabon kakakin majalisar wakilan Najeriya

Sabon kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila.
Sabon kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila. Concise News

Yan Majalisun wakilan Najeriya sun zabi Femi Gbajabiamila na Jam’iyyar APC a matsayin shugaban Majalisar wakilai, yayin da suka zabi Ahmed Idris Wase a matsayin mataimakinsa.

Talla

Wannan ya biyo bayan kaddamar da Majalisar da aka yi talatar nan a Abuja.

Gbajabiamila ya samu kuri’u 281, inda ya kada abokin takararsa, Hon Muhammad Umar Bago wanda ya samu kuri’u 76.

Shi kuwa mataimakin sa Hon Ahmed Idris Wase ya lashe kujerar ce ba tare da hamayya ba.

Wannan nasara tasu, tayi daidai da ta Majalisar Datatwa, inda Sanata Ahmed Lawal ya samu nasarar zama shugaban Majalisa bayan ya kada Sanata Ali Ndume, yayin da Hom Omo Agege ya samu nasara akan Sanata Ike Ikweremadu.

Yanzu haka Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke rike da shugabancin Majalisun guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI