Najeriya

Buhari ya hada kai da gwamnoni don yaki da 'yan bindiga

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na aiki tare da gwamnonin jihohin yankin arewa maso yammacin kasar domin magance masalar hare-haren ‘yan bindiga da ke kashe jama'a babu kakkautawa.

Talla

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a cikin daren da ya gabata wadda ta ce, shugaban kasa ya umarci hukumomin tsaro na tarayya da na jihohi da su fara aiwatar da tsare-tsarensu na samar da tsaro.

Wannan na zuwa bayan harin da aka kaddamar a Tungar Kafau da Gidan Wawa da ke karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, in da mutane 34 suka rasa rayukansu.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, gwamnatinsa ta mayar da hankalinta kan aikin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar, yana mai cewa, gwamnatin ba za ta gaza ba a wannan bangaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.