EU za ta mika rahotonta kan zaben Najeriya ga majalisar dattijai
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yau Talata tawagar kungiyar kasashen Turai da tayi aikin sa ido kan zaben Najeriya, za ta mika rahotonta na karshe da ta tattara kan zabukan kasar, ga sabon shugaban majalisar dattawan kasar sanata Ahmed Lawal.
Rahoton na EU mai kunshe da shawarwari kan kura-kuran da ake bukatar gyarawa, ya zargi Jam’iyyun siyasar kasar, da tinzira tashin hankalin da ya kaiga rasa rayuka da kuma jikkata jama’a.
Zalika rahoton, ya kuma zargi jami’an tsaro da kasa daukar matakan kare lafiyar jama’a da kuma dukiyoyinsu.
A farkon watan nan na Yuni kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch ta ce, hare-hare da tashin hankali sun mamaye zaben shugaban kasar Najeriya da ya gudana a wannan shekara, yayinda ta zargi jami’an soji da 'yan sanda da hannu wajen haddasa matsalolin da aka samu.
Kungiyar ta ce, an samu hare-haren kungiyar Boko Haram da rikicin Fulani makiyaya da manoma da kuma karuwar hare-haren ‘yan bindiga har ma da garkuwa da jama’a a lokacin gudanar da zaben a wasu jihohin kasar.
Zalika kungiyar ta bayyana cewa, ‘yan bindiga sun dirar wa wasu rumfunan zabe tare da kai farmaki kan masu kada kuri’u da ‘yan jarida da masu sanya ido a zaben musamman a jihohin Rivers da Kano.
Human Right Watch ta kuma caccaki jami’an tsaro musamman ‘yan sanda kan yadda suka yi sakaci wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yayin zaben na 2019.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu