Najeriya

"Jana'izar mamata ta lakume sama da Naira biliyan 2 a Bauchi"

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed The Guardian Nigeria

Gwamnatin Bauchi da ke Najeriya karkashin Sanata Bala Mohammed ta ce, tsohon Gwamnan jihar, Mohammed Abubakar ya kashe Naira biliyan 2 da miliyan 300 wajen saya wa mamata linkafani da wasu kayayyakin jana’iza cikin watanni biyar kacal.

Talla

Mai magana da yawun Gwamna mai ci, Dr.Ladan Salihu ya shaida wa manema labarai cewa, an kashe kudaden ne tsakanin watan Janairu zuwa Mayun shekarar bana.

Dr. Salihu ya ce, an kashe sama da Naira miliyan 900 wajen sayen linkafanin mamatan, yayinda aka kashe Naira biliyan 1 da miliyan 400 wajen sayen katakan da ake shinfidawa a cikin kaburbura.

Sai dai tsohon Gwamnan ya musanta zargin wanda ya bayyana a matsayin abin dariya, amma gwamnati mai ci ta ce, tana da shaida akan batun.

Gwamnatin jihar ta kuma kara da cewa, za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an maido  da kudaden talakawan jihar da aka wawure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.