Hukumar NFF na takun saka da yan wasan a Masar
Wallafawa ranar:
Yayin da Najeriya ke shirin karawa da Guinee Conakry a gasar cin kofin Afrika dake gudana a Masar, mai horar da yan Wasan kasar Gernot Rohr ya ce hukumar kwallon kafar Najeriya na takun saka da yan wasan wajen biyan su hakokin su.
Manajan ya ce babu dan wasan da ya karbi kudin alawus din sa na dala 10.000 sakamakon nasarar da suka samu kan Burundi a karshen mako.
Gernot Rohr ya ce wannan na daga cikin dalilin da ya sa Ahmed Musa bai samu isa zuwa ganawa da anema labarai ba,saboda wani taro da yan Wasan suka shiga,wanda ya sa suka yi laittin zuwa atisaye na awa guda.
Matsalar biyanyan wasa hakkokin su na daya daga cikin matsalolin dake hanna ruwa gudu a wasanni a Afrika.
Ta bangaren wasanni,Kamaru na fafatawa da Guinee Bissau,zuwa an jima Kungiyar Jamhuriyra benin za ta ketse reni da Ghana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu