Najeriya

Kwaya ta haukata matasa da dama a Najeriya

Wasu daga cikin nau'ukan kwayoyin da mashaya ke kwankwada
Wasu daga cikin nau'ukan kwayoyin da mashaya ke kwankwada http://togoqueens.com

A kowace ranar 26 ga watan Yuni al'ummar duniya ke bukin yaki da kwankwada da fataucin miyagun kwayoyi da nufin magance matsalar ta'ammuli da nau'ukan abubuwan da ke jefa mutane cikin maye. Masana kiwon lafiya sun ce, ana ci gaba da samun matasan da ke haukacewa saboda shan kwayoyi.Wakilinmu a birnin  Maiduguri, Bilyaminu Yusuf ya duba mana halin da ake ciki game da wannan matsalar a yankin arewa maso gabashin Najeriya.