Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta mallaka wa gwamnatin kasar kudin matar Jonathan

Uwargidar tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, Patience Jonathan
Uwargidar tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, Patience Jonathan Kabir Yusuf
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Lagos na Najeriya ta bayar da umarnin kwace wasu makudaden kudade na uwargidar tsohon shugaban kasar, Patience Jonathan domin mallakawa gwamnatin kasar.

Talla

Kudaden da kotun ta kwace daga hannun Mrs. Jonathan sun hada da Naira miliyan 9.2 da kuma Dala miliyan 8.4 da ake ajiyar su a bankunan Diamond da Fidelity da Eco da Stanbic da Skye da Zenith da First Bank.

Karbe kudaden na zuwa ne bayan lauyan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasar, Rotimi Oyedapo ya gabatar da kudurin kwace kudaden baki daya a gaban Mai Shari’a Mojisola Olatoregun a shekarar 2018.

A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Olatoregun ta ce , babu gamsassun hujjojin da za su hana ayyana wadannan kudaden a matsayin wandanda aka same su ba ta haramtattun hanyoyi ba.

A can baya dai, Hukumar EFCC ta samu izinin wucen gadi na karbe kudaden, yayinda a wannan karo, kotun ta bayar da izinin karbewar din-din-din.

Sai dai a kokarin kare kanta, Uwargida Patience Jonbathan ta bayyana wa kotun cewa, ta samu kudaden ne daga gudun-mawar da wasu mutanen kirki ‘yan Najeriya suka bai wa gidauniyarta a lokacin da mijinta ke kan kujerar mataimakin gwamnan Bayelsa da lokacin da ya zama gwamnan jihar har zuwa lokacin da ya zama shugaban kasa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.