Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin samar da rugagen zamani

Wani filin kiwo a Paiko, da ke jihar Niger a Najeriya.
Wani filin kiwo a Paiko, da ke jihar Niger a Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirinta na Ruga, wanda a karkashinsa za ta samar da filayen kiwo ga makiyaya.

Talla

Matakin ya biyo bayan ganawar kwamitin gwamnatin na Najeriya kan shirin karkashin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sauran masu ruwa da tsaki a yau Laraba.

Gwamnonin da suka halarci taron da Farfesa Osinbajo ya jagoranta, sun hada da Simon Lalong na Filato, Dave Umahi na Ebonyi, sai kuma Atiku Bagudu na Kebbi.

Gwamnatin Najeriya dai na ci gaba da kare shirin nata na gina Rugagen zamani da cewa, shiri ne domin kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar.

Sai dai, shirin takaita zirga-zirgar makiyayan ya ci gaba da haifar da kace-kuce a kasar, in da gwamnonin jihohin yankin kudu maso kudu, da na kudu maso yamma suka yi fatali da shirin na Ruga, yayinda suka bayyana shirin da cewa wani yunkuri na taimaka wa wata kabila da kudaden talakawa.

Kafin daukar matakin dakatar da shirin na ruga da gwamnati tayi, wasu yan kasar sun shirya gudanar da zanga-zangar adawa da shirin ranar 5 ga watan Yuli a garin Abuja.

Yayinda yake yiwa sashin hausa na RFI Karin bayani kan matakin gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu bai bayyana iyakar wa’adin da dakatar da shirin na Ruga zai dauka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.