Najeriya

Kotu ta kwace kayan adon Diezani da darajarsu ta kai dala miliyan 40

Tsohuwar ministar man Najeriya Diezani Alison-Madueke.
Tsohuwar ministar man Najeriya Diezani Alison-Madueke. REUTERS/Rick Wilking/File photo

Wata babbar kotun Najeriya dake Legas, ta bada umarnin kwace kayan adon tsohuwar ministar man kasar Diezani Alison Madueke, da adadinsu ya kai dubu 2, 149 gami da wayarta ta hannu kirar iPhone ta zinare.

Talla

Darajar kayayyakin adon dai ta kai dalar Amurka miliyan 40, kwatankwacin naira biliyan 14 da kusan rabi.

Mai shari’a Nicholas Oweibo ne ya bada umarnin kwace kayayyakin, bisa bukatar hukumar EFCC mai yakar cin hanci da rashawa ta Najeriyar.

Tsohuwar ministar mai Diezani Alison Madueke na fuskantar bincike kan yin sama da fadi da biliyoyin kudade a Najeriya da kuma Birtaniya, inda a yanzu take.

Ko a makon jiya rahotanni sun ce jami’an tsaron kasarta Birtaniya sun ziyarci Najeriya don tattara wasu bayanai kan zarge-zagrgen da ke kan tsohuwar ministar man.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI