Najeriya

Zaben Najeriya: Atiku ya mikawa kotu shaidu dubu 2, 175

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar.
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar. REUTERS/Afolabi Sotunde

Ranar litinin 8 ga watan Yuli, ake sa ran kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya za ta ci gaba da shari’a kan bukatar dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ta soke nasarar lashe zaben watan fabarairu da Muhammadu Buhari na APC yayi.

Talla

Kawo yanzu dai, tsohon mataimakin shugaban kasar ta Najeriya Atiku Abubakar, ya gabatar da shaidu dubu 26, 175 na takardun da ke tabbatar da zargin cewa ta hanyar magudi jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben na shugaban kasa.

Daga cikin shaidun dai, akwai takardun sakamakon kuri’un da aka kada yayin zaben na watan fabarairu, a rumfunan zabe, mazabu da kuma kananan hukumomi, daga jihohi takwas da suka hada Jigawa, Borno, Gombe, Bauchi, Katsina, Kebbi sai Kaduna da kuma Kano.

Tuni dai Mike Igbokwe, Charles Edosomwan dakuma Yunus Usman, lauyoyin wadanda ake kara da suka hada da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, jam’iyar APC da kuma hukumar zabe INEC, suka bukaci yin watsi da shaidun.

Sai dai Lauyan dan takarar jam’iyyar PDP, Livy Uzoukwu, ya shaidawa kotun sauraron karar zaben shugaban kasar cewa, sun shirya tsaf don soma kiran shaidunsu domin yiwa kotun karin bayani kan takardun da suka gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.