Isa ga babban shafi
Najeriya

Buba Galadima ya zama shaidar Atiku na farko a kotu

Shugaban sabuwar jam’iyyar rAPC da ta balle daga APC mai mulkin Najeriya, Buba Galadima.
Shugaban sabuwar jam’iyyar rAPC da ta balle daga APC mai mulkin Najeriya, Buba Galadima. YouTube
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 Minti

Yau litinin, daya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC Injiniya Buba Galadima, ya zama mutum na farko da ya gabatar da shaida gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugabancin Najeriya, kan shari’ar da dan takarar PDP Atiku Abubakar ke kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Talla

Bayan jaddada matsayinshi na shugaban sabuwar jam’iyyar rAPC da ta balle daga APC mai mulki, Buba Galadima ya ce tun lokacin da suka balle, suka kulla yarjejeniya da jam’iyyar adawa ta PDP domin samar da kyakkyawan shugabanci, mai cike da tsoron A ga yan Najeriya.

A lokacin da lauya mai kare shugaban kasa, Wole Olanipekun ya tambaye shi, ko ya san da cewa yarsa na aiki da gwamnatin Buhari, sai Buba Galadima ya kada baki yace, tabbas ya san da haka, hasalima, yar tasa tafi kowa ilimi a gwamnatin, kuma ta taka rawa wajen sake cin zaben gwamnatin.

Galadima, da ya kasance shaida na farko da PDP ta gabatar, ya kuma nanata cewa har yanzu fa shi dan jam’iyyar APC mai mulki ne, domin kawo yanzu babu wanda ya kore shi daga cikinta.

A yau litinin kotun sauraron kararrakin zaben Najeriya ta ci gaba da zamanta, bayan da a karshen makon jiya, dan takarar na Jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gabatar da shaidu dubu 26, 175 na takardun sakamakon kuri’un da aka kada a wasu sassan jihohi 8, da suka hada da Jigawa, Borno, Gombe, Bauchi, Katsina, Kebbi sai Kaduna da kuma Kano, da ke nuna cewa ta hanyar magudi jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben na watan fabarairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.