Najeriya

Mayakan Boko Haram sun yiwa dakarun Najeriya kwanton bauna

Dakarun sojin Najeriya.
Dakarun sojin Najeriya. Reuters

Rahotanni daga Najeriya sun ce mayakan kungiyar Boko Haram sun yiwa sojojin kasar kwanton bauna a Damboa dake Jihar Borno, inda suka kashe 5 daga cikinsu, suka kuma jikkata wasu sama da 10.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa mayakan na Boko Haram sun kaiwa sojojin hari ne lokacin da suka je yankin dokin karkade sauran mayakan da suka rage.

Reuters ta bayyana cewar kwamandan runduna ta 7 ta sojin Najeriya da ke Maiduguri, Janar AbdulMalik Bulama Biu ya tabbatar da artabun da aka yi da dakarunsa, amma yace babu wanda ya mutu daga bangaren sojin Najeriya.

Yayin tsokaci kan farfadowar barzanar hare-haren kungiyar Boko Haram Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya ya bukaci sake dabarun yakin domin samun nasara, a zantawarsa da sashin hausa na RFI.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.