Najeriya

Rahoton musamman kan cika shakaru 10 da rikicin Boko Haram kashi (1)

Tsohon shugaban Kungiyar Boko Haram, Muhammad Yusuf a hannun jami'an sojojin Najeriya
Tsohon shugaban Kungiyar Boko Haram, Muhammad Yusuf a hannun jami'an sojojin Najeriya Daily Post

Yayinda a cikin wannan mako ake cika shekaru 10 da barkewar rikicin Boko Haram a Najeriya wanda ya yi sanadiyar rasa dimbin rayuka da kuma yaduwa zuwa kasashen Nijar da Kamaru da Chadi, Sashen Hausa na RFI zai kawo muku rahotanni na musamman kan rikicin da kuma irin asarar da ya haddasa.

Talla

Ita dai wannan kungiya da ake kira Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati Wal Jihad da ke karkashin shugabancin Muhammadu Yusuf, ta fara arangama ne da jami’an tsaro  da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin 'yan Sanda a watan Yulin shekarar 2009.

A yau Bashir Ibrahim Idris ya duba mana yadda rikicin ya taso daga birnin Maiduguri da kuma matakin da tsohuwar gwamnatin marigayi Umar 'Yaraduwa ta dauka a wancan lokaci.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton.

Rahoto na musamman kan cika shakaru 10 da rikicin Boko Haram kashi (1)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.