Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake yin arrangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan Shi'a

Wani sashi na Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, inda aka yi arrangama tsakanin 'yan sanda da 'yan Shi'a.
Wani sashi na Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, inda aka yi arrangama tsakanin 'yan sanda da 'yan Shi'a. Gulf Times
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 min

Akalla ‘ya’yan kungiyar ‘yan uwa Musulmi IMN da aka fi sani da Shi’a guda 6 ne suka rasa rayukansu a Najeriya, ciki har da mataimakin kwashinan 'yan sanda yayin arrangama da da jam’an tsaron a Abuja babban birnin kasar.

Talla

Wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya tabbatar da ganin gawarwakin 6, yayin Karin bayani kan yadda lamarin ya auku a wannan litinin.

Rahotanni sun ce kafin tashin hankalin, da misalin karfe 12 na rana, ‘yan kungiyar ta Shi’a suka soma gudanar da zanga-zanga a birnin na Abuja don neman sakin shugabansu da ke tsare Shiekh Ibrahim Zakzaky.

Bayan isa gaf da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ne, ‘yan sanda suka yi kokarin dakatar da zanga zangar, matakin da ya wani gungu daga cikin ‘yan kungiyar ta ‘yan uwa Musulmi cinnawa ginin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da ke kusa wuta, abinda yayi sanadin konewar dukiya da aka kiyasta darajarta ta kai akalla naira miliyan 200.

Tashin hankalin baya bayan nan daya ne daga cikin jerin irin arrangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaron Najeriya da ‘yan kungiyar Shi’a yayin zanga-zangar neman a saki shugabansu Shiekh Ibrahim Zakzaky da ke tsare tun a watan disamba na shekarar 2015, bayan arrangamar da aka yi tsakanin mabiyansa da sojoji a garin Zaria.

A baya bayan nan, babbar kotun Najeriya ta bada marnin sakin malamin amma gwamnati ta noke sakamakon sabbin zarge-zargen da ta bijiro da su kansa.

Tun daga shekarun 1970 Shiekh Zakzaky ya soma sa kafar wando daya da gwamnatin Najeriya, bayan da ya bukaci komawar kasar kan tsarin mulki irin na kasar Iran, wanda ta koma bayan gudanar da juyin juya hali a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.