Najeriya

'Yan bindiga sun sace Turkawa hudu a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun sace Turkawa hudu a jihar Kwara ta Najeriya
Wasu 'yan bindiga sun sace Turkawa hudu a jihar Kwara ta Najeriya Jakarta Globe

Bayanai daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu Turkawa hudu da ke aiki a wani kmafanin gine-gine a jihar Kwara.

Talla

Majiyoyi sun ce ‘yan bindiga shida ne suka afka wa Turkawan a wata mashaya da ke wani kauye mai suna Gbale, labarin da kakakin ‘yan sandan jihar DSP Ajayi Okasanmi ya tabbatar da ingancinsa, sannan ya ce suna aiki tukuru domin ceto mutanen.

An bayyana Turkawan da Yasin Colak mai shekaru 33 da Senerapal mai shekaru 40 da Ergun Yurdakul mai shekaru 35 da kuma Seyit Keklik mai shekaru 25, kuma an sace su da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar da ta gabata.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin garkuwa da bakin na kasar waje.

Sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa ba sabon abu bane a Najeriya, matsalar da ta zama ruwan dare game duniya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.